Armenia-Azerbaijan

Armenia da Azerbaijan sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Armenia da Azerbaijan sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ta shirya don kawo karshen rikicin da suka shafe makonni suna yi a kan yankin Nagorno-Karabakh a yau Talata, bayan wasu jerin nasarori da Azerbaijan ta samu a kokarin da take na karbe yankin.

Shugaban Azerbaijan Ilham Heydar Oglu Aliyev (hagu) da na Armenian  Serzh Sargsyan.
Shugaban Azerbaijan Ilham Heydar Oglu Aliyev (hagu) da na Armenian Serzh Sargsyan. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Sa’o’i bayan tsagaita wutar, daruruwan dakarun kiyaye zaman lafiya na Rasha ne suka kama hanyarsu ta zuwa yankin na Karabakh, wanda ya kwace daga ikon Azerbaijan a yayin wani yaki a cikin shekarun 1990s.

Sai dai wannan yarjejeniya ta harzuka wasu Armeniyawa, inda suka fito zanga zanga cikin fushi suka dunguma zuwa shelkwatar gwamnatin yankin suka yi ta farfasa tagogi.

Wasu dimbim mutane ma sun nufi ginin majalisar dokokin kasar su na neman Firaminista Nikol Pashinyan, wanda ya bayyana shiga yarjejeniyar a matsayin abin takaici a gareshi saboda rashin zabi ya yi murabus.

Firaministan ya ce ya shiga yarjejeniyar ce duba da halin da sojin kasar ke ciki na rauni.

Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya ce lallai babu wani zabi da rage wa Mr. Pashinyan.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da cewa dukkanin bangarorin sun amince da tsagaita wuta kacokan, wanda zai samar da yanayi na sulhu mai dorewa.

Putin ya ce za a bar mutanen da rikicin ya daidaita su koma yankunansu, kuma za a yi musayar fursunoni da gawarwaki na mutanen da aka kashe yayin yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI