Faransa-Macron

Macron zai dauki nauyin taron Tarayyar Turai kan ta'addanci

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai dauki nauyin taron kungiyar Tarayyar Turai a da za a yi ta kafar bidiyo a yau Talata, taron da zai duba irin matakan da kungiyar ke dauka dangane da hare haren baya bayan nan da aka kai nahiyar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Photo by Ludovic Marin, Pool via AP
Talla

Shugaba Macron zai fara ganawa ne da shugaban gwamnatin Australia, Sebastian Kurz a birnin Paris, inda daga bisani shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ta hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen za su hade a taron ta kafar bidiyo, kamar yadda fadar Elysee ta bayyana.

Taron na zuwa ne mako guda bayan da wani mai goyon bayan kungiyar IS da ya yi zaman gidan kaso ya kashe mutane hudu a lokacin da ya bude wuta kan mai uwa da wabi a birnin Vienna.

Harin na Vienna ya biyo bayan wanda aka kai wani coci a birnin Nice na Faransa ne a watan da ya gabata, da kuma fille kan wani malamin tarihi Samuel Paty a kusa da birnin Paris.

Fadar gwamnatin ta Faransa ta ce mahalarta taron na Talatar za su amsa tambayoyi yayin wani taron manema labarai da za a yi ta kafar bidiyo.

Faransa ta sha fama da hare haren da ta zargi masu tsatsauran ra’ayin Islama da aikatawa wanda ya sa gwamnatin kasar ta fara daukar matakan fadada hanyoyin sanya wa kungiyoyin addini ido, musamman ma kan abin da ya shafi tallafin kudade da suke samu daga waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI