Amurka-Zabe

Sakataren shari'ar Amurka ya bada umurnin binciken zargin magudi

Sakatrenn shari'a na Amurka William Barr.
Sakatrenn shari'a na Amurka William Barr. REUTERS/Joshua Roberts

Sakataren Shari’ar Amurka William Barr ya bada umurnin gudanar da bincike kan zargin tafka magudin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da ya gudana, wanda Joe Biden ya kada shugaba Donald Trump.

Talla

A wasikar da ya rubutawa Antony-Janar Janar na Jihohi, Barr wanda na hannun damar shugaba Donald Trump ne, ya ce duk da cewa babu wata shaidar da aka tabbatar dangane da zargin, ana bukatar gudanar da bincike a kai.

Manufar dokar shari’a ba ta amince gwamnati ta sa baki a a harkar zabe ba har sai an kammala kintsawa da kidaya kuri’u.

Barr ya shaida wa lauyoyin cewa idan har suka ga wani abin da ya gurbata zaben, kuma zai iya sauya sakamakon zaben na ranar Talata, toh kada su yi kasa a gwiwa wajen bincikar sa sau da kafa.

Umurnin Barr na zuwa ne a yayin da Trump ke fadi – tashin ganin ya kalubalanci nasarorin da Biden ya samu a wasu jihohi masu mahimmanci kamar su Pennsylvania, Nevada, Georgia da Arizona, wadanda su suka ba shi isassun manyan kuri’un da suka kai shi ga nasara.

Kwamitin yakin neman zaben Trump sun shigar da kara a jihohi da dama da zummar canza sakamakon ko kuma tilasta sake kirga kuri’u a wasu jihohi.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce shugaban sashen shari’a dake kula da kararrakin zabe, Richard Pilger ya aje mukamin sa saboda umurnin William Barr.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.