Barayi sunyi awon gaba da Euro miliyan 6 da rabi a wani ofishi a Jamus

Kudin Turai Turai Euro
Kudin Turai Turai Euro Getty Images

Masu bincike a Jamus sun kadamar da farautar wasu mutane 3 da ake zargi da yin awon gaba da zunzurutun kudi har Yuro miliyan 6 da rabi, bayan da suka fasa wani ofishin hukumar shige da ficen kasar.

Talla

A wata sanarwar da hukumar ‘yan sandan Birnin Duisburg ta fitar ta ce barayin sun yi amfani da kwarewa wajen fasa ofishin, inda suka sa na’urar sassakar kankare wajen huda dakin ajiyar kudi.

Har yanzu dai ba a san ko su waye wadannan barayi ba, lalube dai ake ko za a yi katari wajen damke wadannan mutane ‘yan uwan su ‘Da’u fa'ataken dare’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.