Barcelona zata gurfunar da Neymar gaban kotu saboda kudaden da ta biya shi a baya

Kungiyar Barcelona tace zata gurfanar da Neymar a gaban kotu saboda abinda ta kira biyan sa kudaden da suka wuce kima da suka kai Dala miliyan 12 lokacin da yake bugawa kungiyar wasa.

Dan wasan PSG, Neymar.
Dan wasan PSG, Neymar. RFI/Pierre René Worms
Talla

Jaridar El Mundo da ake wallafawa a Spain ta ruwaito cewar Neymar da yayi wasa wa kungiyar Barcelona tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017 ya karbi kudaden da suka wuce kima daga kungiyar a matsayin albashi.

Rahotanni sun ce dan wasan na Brazil na daga cikin sahun farko na ‘yan wasan da suka kaucewa biyan haraji a Spain, inda ake bin sa bashin sama da euro 34 da rabi.

Hukumomin Spain na kuma gudanar da bincike kan lokacin da Neymar yaje Barcelona da kuma tafiyar sa PSG.

Wata Kotu a Spain ta bukaci Neymar da ya biya Barcelona euro miliyan 6 da dubu 790,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI