An jikkata jami'an diflomasiyar Faransa a harin makabartar Saudiya

Wani harin Bam ya raunata mutane da dama a birnin jidda na kasar Saudiya, yayin da jami’an diflomasiyar Turai ke gudanar da bukin tunawa da ‘yan mazan jiya da suka mutu a lokacin yakin duniya na farko.

Tsakiyar birnin Jeddah na kasar Saudiya
Tsakiyar birnin Jeddah na kasar Saudiya AP Photo/Hassan Ammar
Talla

Harin da aka kai a wata makabartar da ba ta musulmai ba, ita ce ta biyu da aka kai wa kasar Saudiya cikin kasa da wata guda, adaidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke neman kwantar da hankulan kasashen Musulmai dangane da fifita zanen batanci kan fiyeyyen halitta, annabi Mohammadu wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa wanda tayi Allah wadai da harin, tace an kai shine, kan mahalarta bukin tunawa da kawo karshen yakin duniya na farko, da akeyi duk shekara, wanda ma’aikatan ofisoshin jakadancin kasashe ciki har da na Faransa ke halarta.

To sai dai gwamantin kasar Saudiya batace uffan ba dangane da harin.

A watan da ya gabata, wani dan kasar Saudiyya ya raunata mai gadin karamin ofishin jakadancin Faransa da ke Jeddah da wuka, a ranar da wani mai dauke da wuka ya kashe mutane uku a wata mujami’a dake Nice a kudancin Faransa.

Kuma wannan Fashewar ta makabartar Jedda ma ta zo ne, adaidai lokacin da shugaba Macron ke gudanar da makamaicin wannan buki a birnin Paris na Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI