Facebook da Google sun haramta tallace - tallacen siyasa

Facebook da Google sun haramta tallace - tallacen siyasa.
Facebook da Google sun haramta tallace - tallacen siyasa. AFP/File

Kafafen Facebook da Google sun tsawaita haramcin da suka yi a kan tallace – tallacen da suka shafi siyasa, a daidai lokacin da ake yada bayanan karya da nufin karfafa ikirarin shugaba Donald Trump na cewa an tafka magudi a zaben shugabancin Amurka da ya sha kaye a hannun Joe Biden na jam’iyyar Democrat.

Talla

Wani babban manaja a Facebook Rob Leathern, ya bada sanarwar cewa katafaren kamfanin sada zumuntar zai ci gaba da tsawaita wannan haramcin tallace – tallacen siyasa ne zuwa wani lokaci da da bai bayyana ba har sai an tabbatar sakamakon zaben shugaban Amurka na 3 ga watan Nuwamba.

Shi ma kamfanin Google ya dau mataki makamancin wannan, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito.

Leathern ya tabbatar da cewa wannan haramcin zai hana duk wani abin da ya shafi tallace tallace a game da zabukan majalisar dattawa 2 da aka shirya a Georgia nan gaba.

Sai dai kwamitin yakin neman zaben shiga majalisar dattawa na jami’iyyar Democrat ya nuna rashin amincewa da wannan mataki, inda yake cewa zai kasance tamkar tauye masu zabe a Georgia.

Sanata Kelly Loeffler ta jami’iyyar Republican, wacce take takaran daya daga cikin kujerun majalisar dattawa ma ta yi makamancin wannan martani, inda take cewa Facebook da Google na kokarin dakile damar fadin albarkacin baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.