Faransa

An yi bukin tunawa da wadanda harin Faransa na 2013 ya ritsa da su

An gudanar da jimamin wadanda hare-haren ta'addanci ya hallaka a Faransa shekaru 5 bayan harin ranar 13 ga watan Nuwambar 2015, wanda ya yi sana diyar mutuwar mutane 130, yayin da wasu 350 suka jikkata a Saint-Denis da kuma birnin Paris.

Jami'an kwana-kwana na aikin ceto a lokacin harin ta'addanci na Btaclan a Faransa, 13 ga watan Nunwambar 2013
Jami'an kwana-kwana na aikin ceto a lokacin harin ta'addanci na Btaclan a Faransa, 13 ga watan Nunwambar 2013 REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A ranar 13 ga watan November 2015 ne Faransa ta hadu da harin ta’addanci mafi muni da aka taba kai mata a tarihi, da kuma kungiyar Isis ta yi ikrarin daukar nauyin kai shi.

Hare haren da aka kai a gidan rawwa da waka na Bataclan,da gidajen giya da na abici da dama dake birnin Paris hade kuma da kusa filin kwallon Stade de France,sun yi sanadiya mutuwar mutane 130 wasu kuma 350 suka jikkata.

Shekaru 5 bayan faruwar hare-haren a safiyar yau juma’a an gudanar da shagulgulan nuna jimami, tare da tunawa da wadanda suka tasa rayukansu, sai dai an takaita yawan mutanen da suka halarci bikin nuna jimamin ne, da ya gudana a karkashin jagorancin PM Faransa Jean Castex da ya samu rakkiyar ministocin cikin gida Gerald Darmanin da na shara’a Eric Dupond-Moretti, sakamakon dokar killace jama’a ta yaki da annobar coronavirus.

Shugaban Gwmanatin na Faransa ya aje Falawa a gaban filin kwallon Stade de France, dake anguwar Saint-Denis, kafin ya ziyarci sauran wuraren dake birnin paris inda aka kai hare haren da suka fi daukar rayukan jama a, irinsa mafi muni da kasar ta gani tun bayan yakin duniya na 2.

An dai kamala wannan safiya ta tunuwa da mutanen da suka rasa rayuknasu a karkashin hare haren na ta’addanci ne a harabar kofar gidan rawa na Bataclan.

Kafin zuwa wannan rana ta yau dai, an karfafa matakan tsaro a wadannan wurare da suka zama alamar tashin hankali ta’addanci, alamar da ke tabbatar da cewa barazanar ta’addanci da ake fuskanta a Faransa bata ragu ba, duk da cewa ta sauya salo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI