Amurka

Biden ya lashe jumillar kuri'un 'Electoral Collage' 306

Manyan kafofin yada labaran Amurka sun fitar da alkaluman karshe na kuri’un kwamitin wakilan musamman dake yanke hukuncin karshe kan zaben shugaban kasa wato ‘Electoral Collage’ a turance, inda sakamakon ya nuna dan takarar Democrats Joe Biden ne ya tabbata shugaba mai jiran gado, bayan lashe kuri’un na 'Electoral Collage' 306, yayinda shugaba Trump ya samu 232.

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden
Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden AP Photo/Andrew Harnik, Pool
Talla

Kafafofin da suka hada da CNN da ABC sun ce nasarar Biden ta sake tabbata ne bayanda kidaya ta nuna dan takarar ya lashe kuri’u mafi rinjaye a jihar Georgia, wanda aka share shekaru jam’iyyar Repulican na rike da ita, yayinda shi kuma shugaba Trump ya lashe karin mafi rinjayen kuri’u a jihar North Carolina, nasarar ta kai jumillar kuri’unsa na Electoral Collage zuwa 232.

Tun ranar asabar din makon jiya aka soma taya dan takarar Democrats Joe Biden murnar nasarar zama zababben shugaban Amurka, bayan samun kuri’un Electoral Collage sama da 270, sakamakon lashe kuri’un na jihar Pennsylvania.

Yanzu haka dai Joe Biden ya baiwa shugaba Trump tazarar kuri’u jama’a dubu 14 a jihar Georgia inda ake sa ran sake kidaya kuri’un da aka kada da hannu da ake sa ran kammalawa a makon gobe, biyo bayan ikirarin magudin da shugaba Trump ke da cigaba da nanatawa an yi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI