Faransa-Amurka

Pompeo ya soma rangadin mako 1 a Turai da Gabas ta Tsakiya

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo Mike Segar/Reuters

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa Faransa a yau Asabar, inda zai soma rangadin kwanaki bakwai a tsakanin wasu kasashen Turai da yankin Gabas ta Tsakiya.

Talla

Sai dai wasu masu sharhi na kallon da wuya ziyarar ta Pompeo at yi wani tasiri, la’akari da cewar dukkanin kasashen da ya ziyarta sun taya abokin hamayyarsu na jam’iyyar Democrats Joe Biden murnar lashe zaben Amurka, kayen da har aynzu shugaba mai ci Donald Trump ke cigaba da nanatawa cewa an tafka magudi, tare da shan alwashin kalubalantar sakamakon zaben a shari’ance.

Jim kadan bayan saukarsa a Faransa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya jaddada bukatar kare manufofin karfafa dimokaradiya, ‘yancin dan adam da kuma mutunta dokokin kasa da kasa tsakanin Amurka da Faransa, wadda ya bayyana a matsayin dadaddiyar kawa.

A Amurka kuwa ranar asabar din dubban magoyan bayan shugaba Donald Trump suka gudanar da gangami a birnin Washington, inda suka nuna goyon bayansu ga ikirarin shugaban na cewar an tafka magudi a zaben shugabancin kasar da ya gudana a farkon watan nan, da alkaluma suka nuna ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa Joe Biden na jam’iyyar Democrats.

Shugaba Trump tare da ayarin motocinsa ya jinjinawa masu gangamin na mara masa baya, sai dai ya rika daga musu hannu ne yayin wucewa ba tare da ya fito daga mota ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.