Zaben Amurka: Trump ya fara nuna alamun mika wuya

A karon farko jiya Lahadi, cikin wasu sakawanni da ya wallafa a shafinsa na twitter, shugaban Amurka Donald Trump ya soma nuna alamun amincewa da kayen da ya sha a hannun abokin hamayyarsa na Democrats Joe Biden, a zaben shugabancin kasar da ya gudana a farkon watan nan.

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Cikin sakon da shugaba Trump ya wallafa ta shafinsa na twitter a jiya Lahadi, ba tare da ambatar sunan Biden ba, ya ce “ya yi nasara”, abinda Trump din bai taba fada ba a bainar jama’a.

Sai dai shugaban na Amurka ya ce nasarar da jam’iyyar Democrats ta samu a zaben shugabancin na Amurka a idanun kafafen yada labarai ne kawai, inda ya dage kan cewa lallai akwai magudi a zaben.

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kasar na farkon watannan ne bayan samun mafi rinjayen kuri’u a jihohin Michigan, Wisconsin, da Pennsylvania wadanda suke da yawan kuri’un ‘Electoral Collage’, wakilan dake yanke hukuncin karshe kan zaben shugaban kasa, nasarar da ta baiwa Biden damar samun sama da kuri’un na ‘Electoral Collage’  270, baya ga jumillar kuri’un gama gari miliyan 77, yayin da Trump ya samu miliyan 72.

A ‘yan kwanakin nan dai Trump ya soma nuna alamun mika wuya da kayen da ya sha a hannun Biden, inda a baya bayan nan yayin jawabi kan rigakafin annobar corona Trump din ya ke cewa ba za sake killace daukacin al’ummar Amurka ba don  dakile cutar, to amma wa ma ya sani ko ba gwamnatinsa bace za ta ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI