Wasanni

Faransa ta doke Sweden 4 -2

Faransa ta doke Sweden da ci 4 da 2 a gasar cin kofin nahiyoyi Turai,duk da cecce –kuce da aka samu kafin soma wasar, biyo bayan ra’ayin wasu daga cikin ma’abuta kwallon kafa da suka bukaci mai horar da kungiyar kwallon kafar Faransa Didier Deschamps ya cire sunayen wasu yan wasa da suka hada da Kylian Mbappe a wannan wasa sabili da raunin da dan wasan ke fama da shi.

Dan Wasan Faransa  Kylian Mbappé.
Dan Wasan Faransa Kylian Mbappé. TT News Agency/Christine Olsson
Talla

Mataimakin mai horar da kungiyar kwalllon kafar Sweden Peter Wettergren,ya sheidawa manema labarai cewa kungiyar Sweden ta taka rawar a zo a gani, sai dai a yi maganar rashin sa’a.

Mai horar da kungiyar ta Sweden ya bayyana kungiyar Faransa a matsayin kungiyar da ta san abinda take yi, ta kuma lakanci kwallon kafa tun fil a zal.

A karshe Peter Wettergren ya na mai cewa indan gaba ta ki, za su rugunmi kadara, itace ta nuna jajircewa don nemo tikitin shiga gasar cin kofin Duniya nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI