Faransa

Kotun Faransa ta baiwa gwamnati wa’adin watanni 3 don kawo sauyi a yaki da dumamar yanayi

Wata Babbar Kotu a Faransa ta baiwa gwamnatin kasar wa’adin watanni uku domin ganin ta fayyace gundarin kokorinta na yaki da dumamar yanayi.

Iska mai guba dake gurbata yanayi
Iska mai guba dake gurbata yanayi REUTERS
Talla

A wani hukunci da masu fafutukar kare muhalli suka yaba a matsayin mai dimbin "tarihi", babbar kotun dake kula da ayyukan gwamnati a Faransa ta baiwa hukumomin kasar wa'adin watanni uku domin ta fayyace mata irin matakan da take dauka dangane da alkawuranta kan dumamar yanayi.

Tun a farkon wannan shekara ne dai, magajin garin Grande-Synthe, daga jam’iyyar masu rajin kare muhalli, Damien Carême wanda yanzu haka yake Majalisar Tarayyar Turai, ya shigar da kara gaban kotun na Faransa cewar, karamar hukumarsa dake arewacin Teku na fuskantar barazana saboda rashin daukar kwararan matakai daga gwamnati.

Kotun wacce ta yanke hukunci kan raunin manufofin gwamnti kan yaki da canji da dumamar yanayi, tace gwamnatin da tayi ruwa da tsaki wajen kasancewa ja gaba kan yarjejeniyar yanayi ta shekarar 2015 da kasashen duniya, amma ta gaza tabuka komai a cikin gida dangane da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI