Faransa

Faransawa na adawa da sabuwar dokar tsaro da majalisa ta amince

Masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tsaro a Faransa
Masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tsaro a Faransa AP Photo/Michel Euler

A cikin wani yanayi mai tsarkakiya Majalisar Dokikin Faransa ta kada kuri’ar amincewa da sabon kudirin dokar tsaro da gwamnati da gabatar wadda za ta haramtawa kafofin yada labarai da sauran masu amfani da shafukan sadarwar zamani yada hotunan jami’an ‘yan sandan kasar yayinda suke gudanar da ayyukansu.

Talla

Amincewa da wannan kudiri a matsayin doka, na da nufin yanke hukuncin daurin shekara guda tare da biyan tarar euro dubu 45 kan duk wanda aka samu da laifin yada hotunan ‘yan sandan Faransa da ka iya haifar musu da fuskantar cin zarafi.

Masu adawa da kudurin sun bayyana shi a matsayin barazana ga manema labarai da sauran kungiyoyin kare hakkin dan adam ta hanyar dakile damar da suke da ita na fallasa rahotannin jami’an tsaron dake aikata laifuka.

Yanzu haka kungiyoyin kare hakkin bil'adama da na 'yan jaridu ciki harda RFI na shirin gudanar da zanga-zanga a birnin Paris, domin nuna adawa da sabuwar dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.