An gudanar da zanga - zangar adawa da dokar tsaron kasa a Faransa

Dubban mutane ne suka yi tattaki a biranen Faransa don zanga zangar nuna rashin amincewa da dokar da za ta haramta daukar hotunan jami’an ‘yan sanda yayin da suke gudanar da aikinsu, matakin da ake caccaka a matsayin tauye hakkin ‘yan jarida.

Yadda masu zanga zang suka fito a biranen Paris. (misali)
Yadda masu zanga zang suka fito a biranen Paris. (misali) . REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

An yi taron masu zanga zanga mafi girma, mai mutane dubu 7 a kusa da hasumiyar Eifel, wato Eifel Tower, inda ‘yan sanda suka sa ido, amma kuma da ‘yar kwarya – kwaryar kai – ruwa – rana da masu zanga zanga bayan taron.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa jimillar mutane dubu 22 ne suka fito wannan zanga zangar a fadin kasar da suka hada da wakilan kafofin yada labarai da na masu gwagwarmayar ‘Yellow Vest’.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne majalisar dokokin Faransa ta amince da kwaskwararren dokar tsaron kasa, wacce ta tanadi hukunci mai gauni ga duk wanda ya dauki hoton ‘yan sanda yayin gudanar da aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI