Taron G20 ya karkata kan wadata rigakafin Covid 19 a duniya

Taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20, wanda Saudiya ke karbar bakuncinsa ya jaddada bukatar ganin an wadata duniya da allurar rigakafin cutar coronavirus.

Sarki Salman na Saudiya, mai karbar bakuncin taron G20 na 2020.
Sarki Salman na Saudiya, mai karbar bakuncin taron G20 na 2020. VIA REUTERS - BANDER ALGALOUD
Talla

Shugabannin kasashen G20 ciki har da Donald Trump na Amurka wanda ya ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasar da ya gudana a farkon wannan wata sun bayyana a kwallaben talabijin a babban taron kafar intanet da ke gudana a yanayi na annobar coronavirus.

Taron na yini biyu ta kafar bidiyo wanda ke gudana tun a jiya Asabar, shine irinsa na farko da wata kasar Larabawa ke daukar nauyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI