Wasanni

Liverpool ta kafa sabon tarihi ba tare da zaratan 'yan wasanta ba

'Yan wasan Liverpool da City yayin fafatawa
'Yan wasan Liverpool da City yayin fafatawa Clive Brunskill/Reuters

Kungiyar Liverpool ta dare mataki na biyu kan teburin gasar Premier ingila, biye da Tottenham da maki 20-20 ko wannensu, inda ta dakile fatan Leicester City na zuwa saman teburin, bayan kwazo da ta nuna da kuma samun nasarar ci 3 da nema a Anfield.

Talla

Bangaren na Jurgen Klopp ya ci gaba da kasancewa a biye Spurs da bambancin kwallaye, amma yanayin nasarar ya zama abin gargadi ga masu fatan kwace kambin daga hannun zakarun na Primiya.

Liverpool ta kuma kafa sabon tarihi a kulob din na fafata wasanni 64 a gasar cikin gida ba tare da an doke ta ba, wanda hakan ya karya tarihinsu na baya.

Kuma sun samu wannan nasarar ce a cikin matsanaicin halin rashin ‘yan wasansu irinsu, Virgil van Dijk, Trent Alexander-Arnold, Joe Gomez, Jordan Henderson, Thiago Alcantara da Mohamed Salah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.