Faransa

Faransa na neman shawara kan fita daga kangin bashi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Firaminista  Jean Castex yayin wata ganawa a fadar Elysee.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Firaminista Jean Castex yayin wata ganawa a fadar Elysee. AP Photo/Thibault Camus, Pool

Gwamnatin Faransa ta sanar da kafa wani kwamitin kwararru a fannin tattalin arziki wanda zai taimaka mata da shawarwari kan yadda za ta warware basukan da suka dabaibaye ta na kudin da ta yi amfani da su wajen farfado da kasuwancin da Covid-19 ta kassara a kasar.

Talla

Ministan kasafin kudin Faransar Olivier Dussopt da ke sanar da wannan mataki ya ce tuni kwararrun da masana kasuwanci a matakai daban-daban da kuma gogaggu a fannin hada-hadar kudi suka hallara don baje kolin shawarwarinsu ga gwamnatin ta Faransa a wani yunkuri na lalubo hanyoyin da kasar za ta bi don fita daga basukan da suka dabaibayeta.

Cikin kwararrun bayanai sun ce har da fitaccen masanin tattalin arzikin nan Beatrice Weder di Mauro wanda ya shawarci shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan yadda ta shawo kan matsalar tattalin arzikin da ta tunkaro kasarta a baya.

Shugaban kasar ta Faransa, Emmanuel Macron tsohon kwararren ma’aikacin banki ya ce yana kokarin kaucewa haraji wajen dawo da makudan kudaden da suka yi amfani da shi a farfado da kasuwancin da Covid-19 ta tagayyara a cikin kasar.

Faransa dai ta sanar da shirin zuba yuro biliyan 460 don farfado da fannonin da annobar ta Covid-19 ta tagayyara bayanda ta tilasta kulle hada-hadar kasuwanci da cinikayya tun daga tsakiyar watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.