EU-Birtaniya

Turai ta ki kulla yarjejeniyar kasuwancin da Birtaniya

Zauren Majalisar Dokokin Turai da ke birnin Brussels.
Zauren Majalisar Dokokin Turai da ke birnin Brussels. REUTERS/Francois Lenoir

Majalisar Dokokin Kungiyar Tarayyar Turai ta ki amincewa da sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwancin da ake shirin kullawa tsakanin mahukuntan London da na EU bayan ficewar Britaniya daga kungiyar.

Talla

Cikin sakon da ya wallafa a Twitter, Bernd Lang, shugaban kwamitin kasuwanci a Majalisar ya ce dole samar da doka ta daban dangane da kasuwancin tsakanin EU da Birtaniya matukar ana bukatar sahalewar majalisar.

A cewar Mr Lange da ke wakiltar Jamus a majalisar rawar da Firaminista Boris Johnson ke takawa ce ta kaisu halin da suke ciki a yanzu kuma sanya hannu kan yarjejeniyar na matsayin kwaba matukar aka ci gaba da tafiya a yadda ake.

Shima Mr Manfred Weber shugaban gungun ‘yan majalisun turai masu ra’ayin rikau ya ce wajibi yiwa yarjejeniyar tsayin daka don kaucewa fadawa matsala.

Zuwa yanzu dai kasa da kwanaki 40 ya ragewa Birtaniya ta kammala tsare-tsaren raba gari da EU kamar yadda aka tsara nan da ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa da suka kunshi yarjeniyoyin kasuwanci, tsaro da cinikayya, baya ga alakar iyakokinta da na sauran mambobin EU gabanin bankwana da kungiyar dungurugum a ranar 31 ga watan Janairun 2021.

An dauki lokaci mai tsawo ana kai ruwa rana tsakanin kungiyar ta EU da Britaniya kan yadda huldar kasuwanci za ta ci gaba da kasancewa tsakaninsu bayan sun raba garin da ma yadda ita Birtaniyar za ta biya wasu hakkoki da suka rataya a wuyanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.