Shugabancin EU ya gana da zababben shugaban Amurka Joe Biden

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Joe Biden.
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Joe Biden. AP Photo/Andrew Harnik

Shugabannin manyan hukumomin kasashen Turai guda biyu sun gana da zababben shugaban Amurka Joe Biden inda suka gayyace shi wani taro na musamman da zai gudana a Brussels a shekara mai zuwa.

Talla

Shugaban Majalisar Turai Charles Michel da shugabar gudanarwa Ursula von der Leyen sun bayyana aniyar su ta aiki tare da Biden domin dinke duk wata barakar da aka samu tsakanin Yankin da Amurka a karkashin jagorancin Donald Trump.

Shugabannin biyu sun taya Biden murnar gagarumar nasarar da ya samu a zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.