Dole ne mu kauce wa sake barkewar corona-Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Photo by Ludovic Marin, Pool via AP

Gwamnatin Faransa ta ce za ta kawo karshen dokar kulle ta yaki da cutar corona nan da ranar 15 ga watan gobe, sannan daga ranar Asabar mai zuwa za a sake bude shaguna domin ci gaba da harkokin kasuwanci, yayin da shugaban kasar Emmanuel Macron ya bayyana cewa, dole ne su yi duk mai yiwuwa wajen kauce wa sake barkewar annobar.

Talla

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, shugaba Emmanuel Macron ya ce daga ranar 15 ga watan gobe, dokar hana fita za ta fara aiki ne daga karfe 9 na dare zuwa karfe 7 na safiya amma ban da yammacin 24 da 31 da za a yi bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

A wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar ta kafar talabijin, shugaba Macron ya ce ,“Faransawa maza ta Mata, ya ku ‘yan uwana, idan baku manta ba, 28 ga watan Oktoba da ya gabata na yi muku alkawarin ci gaba da bayyana muku halin da ake ciki dangane da annobar corona da kuma irin matakan da muke dauke, wata daya kenan, wani ci gaba muka samu".

"Adadin wadanda ke kamuwa da cutar kullu yaumin ya ragu matuka, da farko muna samun sama da mutane 60 da suke kamuwa, amma daga makon da ya gabata ya ragu zuwa kasa da dubu 20, wannan yana nufin cewa mun fice daga barkewar cutar corona karo na biyu, wannan nasara ce tamu baki daya a kokarin da muka yi da ku". Inji Macron.

Shugaban ya kuma yi kira ga Faransawa da su kaurace wa tafiye-tafiye marasa muhimmanci, kana su ci gaba da mutunta dokar nesa nesa da juna musamman a lokutan bukukuwan Kirismati da bikin sabuwar shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.