Faransa

Faransa za ta tilastawa manyan kamfanonin sadarwa biyan harajin Intanet

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AP Photo/Francois Mori, Pool

Gwamnatin Faransa za ta tilastawa manyan kamfanonin sadarwar na Amurka da su biya harajin yanar gizo daga ribar kudaden da suka samu a bana duk da cewa, hukumomin Washington sun yi barazanar ramuwar gayya kan kayayyakin Faransa ke shigar da su Amurka.

Talla

Ma’aikatar Kudaden Faransa ta ce, tuni aka sanar da wannan matakin karbar harajin ga kamfanonin na Google da Amazon da Facebook da Apple.

Amurka ta ce, ba a yi wa wadannan manyan kafanonin fasahar adalci ba dangane da karbar haraji daga gare su.

Sai dai wannan mataki na Faransa na yin barazana ga dadadden rikicin nan kan yadda manyan kamfanonin na Amurka ke biyan haraji mai yawa a kasashen da suke gudanar da ayyukansu.

A karkashin dokar Kungiyar Tarayyar Turai dai, Kamfanonin na Amurka za su iya bayyana ribar da suke samu daga sassan nahiyar a cikin daya daga cikin kasashen yankin mamba a kungiyar.

Mafi akasari dai, kamfanonin na sanar da ribarsu ne a kasashen na Turai masu karbar karamin haraji irinsu Ireland da Netherlands.

A shekarar 2019 ne Faransa ta kafa sabuwar dokar harajin yanar gizo, inda ta bukaci kamfanonin da su rika biyan kashi uku na ribar kudin da suke samu daga tallace-tallacen intanet.

Sai dai hukumomin birnin Paris sun cimma matsaya da gwamnatin shugaba Donald Trump kan dakatar da wannan dokar harajin, amma a yanzu bisa dukkan alamu sun yi watsi da matsayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.