Faransa

Cin zalin da 'yan sandan Faransa suka yi wa wani bakar fata ya harzuka Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron Fuente: Reuters.

Fin karfin da yan sandan birnin paris suka nuna kan wani mutum bakar fata ta hanyar yi masa dukan kawo wuka, ya yi matukar harzuka shugaba Emanuel Macron, tare da sake farfado da zazzafar mahawarar kabilanci da kuma cin zarafin yan sanda kan fararen hula a Faransa.

Talla

Hotunan bidiyo dai sun nuna Michel Zecler, wani mai sana’ar kida da waka, bakar fata, wasu ‘yan sanda farar fata su hudu, sun mai rubdugu, suna lakada mai duka a birnin, gab da kofar shiga masana’antarsa ta kida dake birnin paris a ranar Asabar da ta gabata.

Hoton da shafin yanar gizon Loopsider ya yada a jiya Alhamis, ya haifar da bacin rai sosai a kasar, har zuwa tsakananin mahukumta, da kuma wasu fitattun ‘yan wasan motsa jiki a kasar ta Faransa.

fadar shugabancin Faransa a yau Juma’a ta ce shugaban, Emanuel Macron ya yi matukar harzuka da ganin bidiyon.

Martanin farko da ya fito daga mahukumtan ya kasance kan gaba a cikin kanun labaran da jaridun kasar suka wallafa a yau Juma’a.

" Tashin zuciya", ita ce Kalmar da jaridar Liberation ta rubuta kan hoton fuskar Michel Zecler da ta kumbura sanadiyar dukan da ya sha, a yayin da ita kuma jaridar Le Monde ke cewa laifin mahukumta ne

shahararun yan kwallon kafar kasar ta faransa irinsu Antoine Griezmann da Kylian Mbappé duk sun nuna matukar bacin ransu da abkuwar lamarin ta shafukan sada zumunta.

Gerald Darmanin, ministan cikin gidan kasar ta Faransa dake shan suka sakamakon sauye sauyen tsaro da yake bullowa da su ba tare da lissafi ba, a jiya Alhamis ya yi wata ganawa da shugaba Macron da ya bukace shi da ya dau matakin ladabtarwa kan yan sandan kamar yadda majiyar gwamnatin kasar ta sanar.

Bayan ganawar ta su ce ta kafar talabijin din France 2 ministan ya bada umarnin tubewa tare da dakatar da yan sandan 4 da aka gurfanar ana zarginsu da aikata laifin jefa gurnetin hayaki mai sa hawaye a cikin studion da kuma shafawa kayan sarki na jami’an tsaron jamhuriya kazanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.