Iran

Iran ta ce an kashe mata masanin kimiyar nukiliya Fakhrizadeh

Shugaban Iran Hassan Rohani.
Shugaban Iran Hassan Rohani. REUTERS/Brendan McDermid

Iran ta sanar da cewar an kashe mata masanin kimiyar hada nukiliya Mohsen Fakhrizadeh sakamakon wani kazamin harin da wasu 'yan ta’adda suka kai masa yau juma’a.

Talla

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce Fakhrizadeh ya mutu ne a asibiti sakamakon munanan raunukan da ya samu lokacin da maharan suka kai hari motar sa da kuma musayar wutar da aka samu tsakanin su da masu tsaron lafiyar sa.

Sanarwar ta ce jami’in da ke shugabancin sashen bincike da kirkira na ma’aikatar tsaron Iran ya rasu a asibiti bayan da jami’an kula da lafiya suka kasa ceto rayuwar sa.

Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif ya yi Allah wadai da kisan wanda ya bayyana shi a matsayin harin ta’addanci.

Kasashen yammacin duniya na zargin kasar Iran da yunkurin samar da makamin nukiliya duk da matsayin Amurka da Israila da ke cewa ba zasu taba bari ta samu makamin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.