Turai-Covid-19

Adadin wadanda korona ta kashe a Turai ya zarta dubu 400

Dakin kulawan gaggawa na masu dauke da cutar korona a Brazil
Dakin kulawan gaggawa na masu dauke da cutar korona a Brazil REUTERS

Adadin Mutanen da cutar korona ta kashe a nahiyar Turai ya zarce 400,000, a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta duniya tace mutanen da cutar ta kashe a fadin duniya sun kai miliyan guda da dubu 444,426 daga cikin mutane sama da miliyan 61 da rabi da suka harbu da ita.

Talla

Tuni wasu gwamnatocin kasashen Turai suka dauki matakai daban daban da zummar dakile sake dawowar cutar, cikin su harda kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Spain da kuma Belgium.

A Amurka, birni na biyu mafi girma a kasar, wato Los Angeles ya haramta taron jama’a da na addinai da zanga zanga saboda sake dawowar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.