Wasanni

'Yan wasan Barcelona sun amince a zaftare musu euro miliyan 122 saboda korona

Allon dake wajen filin wasan Barcelona na Camo Nou
Allon dake wajen filin wasan Barcelona na Camo Nou Josep LAGO / AFP

Kungiyar kwallon kafar Barcelona tace ‘yan wasan ta su amince a zabtare musu albashin da ya kai euro miliyan 122 domin kare ta daga durkushewa, sakamakon matsalolin da take fuskanta wadanda suka biyo bayan annobar korona da ta mamaye duniya.

Talla

Kungiyar ta kuma ce ta cimma yarjejeniya da ‘Yan wasan na jinkirta biyan wasu hakkokin su da suka kai euro miliyan 50 zuwa shekaru 3 masu zuwa.

Alkaluman kungiyar sun nuna cewar Barcelona tayi asarar kudaden da suka kai euro miliyan 97, yayin da bashin da ake binta suka kai euro miliyan 488.

Ko a watan Maris da ya gabata, ‘yan wasan kungiyar sun amince da shirin zabtare musu kashi 70 na albashin su sakamakon cutar korona wadda ta hana gudanar da wasanni, matakin da ya taimaka wajen biyan albashin wasu ma’aikatar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.