Wasanni

Babu sauran nishadi a harkar kwallon kafa - Guardiola

Cocin Manchester City Pep Guardiola
Cocin Manchester City Pep Guardiola Reuters/Jason Cairnduff

Babu wani sauran nishadi a harkar Kwallon kafa, inji Cocin Manchester City Pep Guadiola. 

Talla

Guardiola ya bayyana hakan ne duk da nasara mafi girma da City ta yi a kakar bana, na doke Burnley da ci 5-0 a filin wasa na Etihad a ranar Asabar wanda kuma ita nasara ta biyu a gida.

Amma duk da haka Guardiola baiyi cikakken gamsuwa da nasarar ba, wato bai nuna alamun murna ba.

Ya nuna damuwa ne, cewar wasar itace ta 29 a jere da City ke bugawa ba tare da magoya baya ba a cikin filin wasan ba, kuma hakan lamarin zai kasance a akalla wasanni biyar masu zuwa kafin wata kila a samu sauyin, lokacin da kungiyar za ta je Southampton a ranar 19 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.