Wasanni

Bana fargabar kora daga Arsenal - Arteta

'Yan wasan Arsenal a fili cikinsu harda Pierre-Emerick Aubameyang
'Yan wasan Arsenal a fili cikinsu harda Pierre-Emerick Aubameyang REUTERS/David Klein

Mai horar da 'Yan wasan Arsenal Mikel Arteta ya yi watsi da tambayoyin da akayi masa dangane da makomar sa, sakamakon sake shan kashin da kungiyar ta yi a gida daga Wolverhampton Wanderers wanda shine irin sa na 3 a wannan kakar.

Talla

Shan kashin da kungiyar tayi da ci 2-1 ya sanya ta cikin mummunar yanayin da bata taba shiga ba tun daga shekarar 1981, abinda ya sanya kungiyar a matsayi na 14 cikin jerin kungiyoyi 20 dake cikin gasar Firimiya.

Bayan kamala wasan Arteta yace baya fargabar korar shi daga aiki domin kuwa korar wani abu ne da duk wani manaja ke fuskanta idan aka samu akasi lokacin gudanar da aikin sa.

Manajan yace abinda yafi damun sa shine shirya 'yan wasan Arsenal wajen ganin sun bada gudumawar da ta dace, amma batun fargabar kora bata gaban sa.

Masu sanya ido sun zargi irin rawar da kungiyar ke takawa sakamakon rashin jajircewa wajen samun nasara kan abokan karawar su.

Wasu kuma na zargin Arteta da kin yiwa fitaccen dan wasa Mesut Ozil rajistar buga wasannin kakar bana saboda kin yarda ya rage albashin sa duk da yake sun ki sallamar sa daga kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.