Bakin-Haure

Faransa ta ceto bakin haure 64 daga mashin ruwar ta

Wasu baki da aka ceto a gabar ruwan Spain
Wasu baki da aka ceto a gabar ruwan Spain REUTERS/Borja Suarez

Wani Jirgin ruwan Faransa ya ceto bakin haure 64 da suka hada da mace mai ciki da yara kanana da suke kokarin tsallakawa zuwa Birtaniya a wani jirgin ruwa mara inganci.

Talla

Sanarwar da jami’an kula da mashigin ruwan kasar suka gabatar tace an fara ceto baki 45 a ranar asabar kusa da Leffrinckoucke dake gaf da tashar ruwan Dunkirk, yayin da lahadi da safe aka ceto wasu 19.

Yanzu haka an mika su ga jami’an Yan Sanda.

Tuni kasashen Birtaniya da Faransa suka sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya wadda zata hana baki tsallakawa kasashen biyu ta barauniyar hanya sakamakon karuwar yawan bakin da ake samu.

Yarjejeniyar ta kunshi kara yawan sintirin jami’an tsaro daga ranar 1 ga watan Disamba da kuma amfani da jiragen sama masu sarrafa kan su domin gano masu kokarin tsallaka iyakar.

Birtaniya tayi alkawarin bada kudin da ya kai sama da euro miliyan 31 domin taimakawa Faransa gudanar da aikin kamar yadda Sakataren cikin gida Priti Partel ya sanar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.