Coronavirus

Birtaniya ta amince da allurar riga-kafin corona

Birtaniya ta zama kasa ta farko a Turai da ta fara amfani da riga-kafin coronavirus
Birtaniya ta zama kasa ta farko a Turai da ta fara amfani da riga-kafin coronavirus AP Photo/Kirsty Wigglesworth, File

Birtaniya ta za ma kasar Turai ta farko da ta amince da allurar riga-kafin cutar coronavirus da hadin gwiwar kamfanonin Pfizer da BioNTech suka samar, inda gwamnatin kasar ta bada damar soma amfani da maganin a makon gobe.

Talla

Sakataren Lafiyar Birtaniya Matt Hancock ne ya sanar da matakin amincewa da allurar riga-kafin cutar bayan aikin tantance sahihancinta da Hukumar Kula da Ingancin Magunguna Mai Zaman Kanta ta Birtaniya ta yi.

Yayin sanarwar, Hancock ya ce a makon gobe allurar riga-kafin cutar dubu 800,000 da suka yi oda za su isa kasar ta Birtaniya.

Gwajin karshe da aka yi kan maganin riga-kafin da hadin gwiwar Pfizerda BioNTech ya samar a watan Nuwamban da ya kare, ya nuna cewar ingancin allurar ya kai kashi 95 cikin 100 wajen hana kamuwa da cutar coronavirus tsakanin mutane masu yawan shekaru da matasa ba kuma tare da fuskantar wata matsala ba.

Yanzu haka, gwamnatin Birtaniyar ta yi odar allurar riga-kafin annobar ta coronavirus miliyan 40, wadanda za su isa a bai wa akalla mutane miliyan 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.