Faransa

Gwamnatin Faransa za ta yi wa daukacin 'yan kasar allurar rigakafin Coronavirus

Yadda birnin Paris ya kasance a ranar farko daaka sake killace jama'a don dakile annobar Coronavirus a karo na 2, 30/10/2020.
Yadda birnin Paris ya kasance a ranar farko daaka sake killace jama'a don dakile annobar Coronavirus a karo na 2, 30/10/2020. Reuters

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirin gwamnatinsa na gudanar da aikin yi wa mutane alluran rigakafin cutar coronavirus a fadin kasar.

Talla

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban Macron ya ce za a soma aiwatar da shirin alluran rigakafin daga watan Afrilu dake tafe zuwa Yuni

Rigakafin zai soma ne da masu rauni da tsofaffi, kafin ya isa ga sauran al’umma.

Faransa dai na fama yanzu haka da wannan annoba da ta salwantar da rayukan dubban mutane akasarinsu masu yawan shekaru, yayin zangon farko da na biyu da annobar ta barke a kasar.

A makwannin da suka gabata ne kuma alkaluman hukumomin lafiyar kasar suka nuna yadda ake samun adadin masu kamuwa da cutar ta coronavirus a kasar sama da dubu 30 a rana guda, tsawon kusan mako guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.