Coronavirus

Majalisar Birtaniya ta amince da sabbin dokokin takaita walwalar jama'a

Zauren majalisar dokokin Birtaniya dake birnin London
Zauren majalisar dokokin Birtaniya dake birnin London REUTERS

Majalisar Birtaniya ta kada kuri’ar amincewa da daftarin dokokin takaita walwalar jama’a da gwamnatin kasar ta gabatar mata don yakar annobar coronavirus, dokokin da take fatan su maye gurbin dokar killace daukacin al’ummar Ingila ta tsawon wata guda, da ta wa’adinta ya kare a daren jiya.

Talla

‘Yan majalisar Birtaniya 291 ne suka goyi bayan kafa sabbin dokokin takaita walwalar jama’ar, yayin da 78 suka hau kujerar naki, abinda ya baiwa gwamnatin Fira Minista Boris Johnson nasarar soma aiwatar da sabbin matakan yaki da annobar coronavirus a sassan Ingila, da za su maye gurbin dokar kullen da ta shafe wata guda tana aiki miliyoyin mutane.

Majalisar Birtaniyar ta amince da sabbin dokokin dakile annobar ta korona duk da cewa wakilai da dama ciki har da na Jam’iyyar Conservatives mai mulki na adawa da matakan.

Yanzu haka dai bayanai daga hukumomin Birtaniyar sun nuna cewar yayin da birnin London ya tsallake fadawa cikin yankunan da za a tsaurara matakan takaita walwalar jama’a, sama da mutane miliyan 23 a sassan Ingila ne dake rayuwa a yankunan da annobar tafi kamari bayan barkewarta a karo na 2, za su kasance a karkashin sabbin dokokin dakile cutar, ciki har da hana zirga-zirga cikin dare.

Birtaniya na cikin kasashen Turan da annobar corona ta fi yiwa ta’adi, bayan halaka sama da mutane dubu 58 a kasar daga cikin akalla mutane miliyan 1 da dubu 600 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.