Faransa

Faransa ta fara bincikar Masallatai kan zargin koya tsattsauran ra'ayi

Wani babban Masallachi da ke Créteil gab da birnin Paris na Faransa.
Wani babban Masallachi da ke Créteil gab da birnin Paris na Faransa. Reuters/Gonzalo Fuentes

Hukumomin Faransa sun ce daga yau alhamis jami’an tsaro za su fara kaddamar da bincike kan Masallatai da wuraren ibadar da ake zargin cewar ana cusawa matasa tsattsauran ra’ayi sakamakon hare haren da aka samu a kasar.

Talla

Ministan cikin gida Gerald Darmanin ya sanar da haka, inda ya ke cewa duk wani Masallachi ko wurin ibadar da aka samu yana aikata wannan laifi za a rufe shi ba tare da bata lokaci ba.

Binciken da jami’an tsaro za su fara yau ya biyo bayan hare hare guda biyu da aka kai wadanda suka girgiza kasar Faransa da suka kunshi fille kan malamin makaranta da ya nuna hotan batunci ga Manzan Allah tsira da Amincin Allah suka kara tabbata a gare shi da kuma daba wukar da aka yiwa wasu mutane 3 a Majami’ar Nice.

Ministan bai bayyana wuraren ibadar da za a gudanar da bincike akan su ba, amma ya ce akwai 16 a birnin Paris da kuma 60 a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.