Isra'ila ta ce ana barazanar kai wa 'yan kasarta hari a kasashen waje

Benyamin Netanyahu, Fira Ministan Isra'ila.
Benyamin Netanyahu, Fira Ministan Isra'ila. Gali Tibbon/Pool via REUTERS

Isra’ila ta ta ce tana  fargabar ana iya kai wa 'yan kasarta hari bayan da Iran ta sha alwashin daukar fansa a game da kisan masanin kimiyyar Nukiliyarta wanda take zargin ke zargin Isra’ila da aikatawa.

Talla

Ma'aikatar tsaron Isra’ila ce ta fitar da wanan gargadi ga 'yan kasar da ke zaune a kasashen ketare, musaman kasashen da ta ke makwabtaka da su, irin su Iran da ma yankin Afrika.

Hukumomin kasar Isra’ila na cikin fargaba kasancewar bayanai dake fitowa daga kasashen Georgia, Azerbaidjan, Turkiya, Kurdistan, Daular Larabawa da Bahrain. A karshen makon nan ake sa ran ministan harkokin wajen Isra’ila Gabi Ashkenazi zai ziyarci Bahrain,kasa da kusan wata biyu da Isra’ila da Bahrain suka soma dasawa.

Mutuwar masanin kimiyyar Iran ya girgiza kasar matuka.

Mohsen Fakhrizadeh ya mutu ne Juma’ar da ta gabata biyo bayan wani hari da aka kai wa ayarin motocin da ke tafe da shi a birnin Teheran.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani da babbar murya, ya bayyana cewa kasar sa za ta dau fansa, a dai dai lokacin da Firaministan Isra’ila ke zargin Iran da kokarin fadada manufofinta zuwa kasashen Iraki,Yemen da Syria a wannan lokaci da Amurka, ta bakin shugaba mai jiran gado Joe Biden ta bayyana cewa za a sake duba yarjejeniyar nukiliya da kasar ta cimma bayan dawowar Amurka a cikin wannan tafiya.

Ministan harakokin wajen Iran Mohamed Javad Sharif ya yi amfani da wannan dama wajen yin  kira ga shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden na ganin ya cire takukkunman da aka saka wa Iran da jimawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.