Birtaniya-EU

Sarkakiyar tattaunawar kasuwanci tsakanin Turai da Birtaniya ta ta'azzara

Michel Barnier, babban mai tattaunawar Tarayyar Turai kan ficewar Birtaniya daga kungiyar.
Michel Barnier, babban mai tattaunawar Tarayyar Turai kan ficewar Birtaniya daga kungiyar. REUTERS/Francois Lenoir

Shakkun da Tarayyar Turai ke yi a game da cimma yarjejeniyar kasuwancin bayan rabuwa da Birtaniya na dada ta’azzara a yau Juma’a, sakamakon barazanar hawa ‘kujerar naki’ da Faransa ta yi, duk da cewa ana kusan mataki na karshe a tattaunawar da bangarorin biyu ke yi.

Talla

Masu wakiltar Tarayyar Turai da Birtaniya a wannan tattaunawar, Michel Barnier da David Frost sun yi zazzafar muhawwara a game da damar yin su, da dokokin gudanar da kasuwanci da kuma matakan tabbatar da yarjeniyoyin da aka cimma.

Amma ganin yadda lokaci ke kurewa, idan har daga karshe aka cimma yarjejniyar kafin karshen shekara, kuma Birtaniya ta fice daga kasuwar bai daya, abin ba zai yi wa manyan kasashen Turai da dama dadi ba, duba da yadda aka jiyo ministan harkokin Turai na Faransa, Clement Beaune yana cewa, idan har aka cimma yarjejeniyar da ba ta da armashi, tabbaci hakika kasarsa ba za ta yi na’am da ita ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani jami’in diflomasiyya a Turai yana cewa, Netherlands da Spain da Denmark na da irin ra’ayin Faransa, na cewa gaggawar karkare wannan tattaunawa don cimma yarjejeniya za ta baiwa Birtaniya damammakin da za su cutar da su.

Sai dai ya zuwa yanzu, kan manyan kasashen Turan a hade yake  a game da baiwa jagoran tattaunawar Michel Barnier goyon baya, ganin yadda suka raba dare da takwaransa na Birtaniya David Frost wajen tatutaunawar cimma yarjejeniya, a yayin da Firaminsita Boris Johnson ke fuskantar zabin da ke gabansa na ko ya mika wuya ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.