Birtaniya da Tarayyar Turai sun tashi baram baram a tattaunawar kasuwanci

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. AP/Olivier Hoslet/Pool

An tashi ba tare da cimma yarjejeniya ba a tattaunawar kasuwanci da ta gudana tsakanin Birtaniya da Tarayyar Turai a jiya Juma’a, lamarin da ya sa masu shiga tsakanin suka mika aikin lalubo mafita ga Firaministan Birtaniya, Boris Johnson da shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Talla

Jagororin biyu za su gana ta wayar tarho a wannan Asabar bayan da after their envoys Michel Barnier da David Frost suka shafe dare da rana suna tattaunawa ba tare da cimma matsaya ba.

Ana sa ran Barnier ya bar birnin Landan, kuma zuwa tsakar ranar Asabar jagorar Turai da Fira minista Boris Johnson za su gana ta wayar tarho.

Ana ta kwan gaba kwan baya a wannan tattaunawar har na tsawon watanni 8, duk da cewa wa’adin barin Turai na Birtaniya ko da yarjejeniyar kasuwanci ko akasi na ranar 31 ga watan Disamba na karatowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.