Samun allurar rigakafi ba ya nufin an murkushe Korona - WHO

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS/Denis Balibouse

Hukumar lafiya ta duniya ta ce samun allurar rigakafin annobar Covid 19 ba yana nufin an shafe cutar daga doron kasa ba ne.

Talla

Hukumar ta yi gargadin cewa kada a yi sake, tana mai cewa ba gaskiya bane cewa don ana daf da fara allurar rigakafi an kawar da matsalar kenan.

A wani taron kafar bidiyo, daraktan taimakon gaggawa na hukumar Michael Ryan ya shaidaa wa mahalarta taron cewa ba rigakafi ne kadai zai magance cutar ba.

A ranar Larabar da ta gabata, Birtaniya ta kasance kasa ta farko da ta amince da amfani da rigakakfin a ilahirin kasar, lamarin da ya kara matsin lamba a kan sauran kasashen duniya su bi sahu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.