Morocco ta shiga jerin kasashen da suka amince da Isra'ila - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kasar Morocco a matsayin kasar Larabawa ta 4 da ta amince da kasar Israila, abın da ya sa Amurkar ta amince da Moroccon a matsayin wadda ta mallaki yankin Yammacin Sahara da ake rikici a kai.

Talla

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya sanar da kulla yarjejeniyar diflomasiya takanın kasashen biyu, wato Morocco da Israila a cigaba da yunkurin ganin kasashen larabawa sun amince da ita, kuma an kawo karshen rikicin da ke Gabas ta Tsakiya.

Wannan ya nuna cewar yanzu haka kasashen Larabawa 4 da suka hada da Daular Larabawa da Bahrain da Sudan da kuma Moroccon sun amince da kafuwar kasar Israila a karkashin shirin da aka yi wa suna ‘yarjejeniyar Abraham’.

Sakamakon wannan cigaba da aka samu, shugaba Trump ya bayyana cewar ita ma kasar Amurka ta amince da Yankin Yammacin Sahara da ake rikici a kai a matsayin Yankin kasar Morocco.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya nan take ta sanar da cewar babu abin da ya sauya dangane da matsayin ta kan Yankin Yammacin Sahara wanda yanzu haka dakarun ta ke aikin samar da zaman lafiya a can.

Ita ma kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta yi Allah wadai da matakin da kasar Morocco ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.