Turai

EU za ta tsaurara matakan sa ido kan kamfanonin sadarwar zamani

Wasu daga cikin shugabannin kungiyar kasashen Turai EU yayin taro a birnin Brussels
Wasu daga cikin shugabannin kungiyar kasashen Turai EU yayin taro a birnin Brussels POOL / REUTERS

Kungiyar tarayyar Turai EU ta soma shirin samar da wata sabuwar dokar sa ido kan yadda manyan kamfanonin sadarwar zamani na duniya ke gudanar da ayyukansu.

Talla

Dokar za ta kuma bada damar yanka tarar da za ta iya kaiwa kashi 10 cikin 100 na jarin kamfanonin muddin suka karya dokokin hamayyar kasuwanci a nahiyar kamar yadda wasu majiyoyi a kungiyar suka sanar da AFP.

Tara, rufewa da kuma haramta gudanar da ayyuka, na daga cikin matakan da kungiyar tarayyar turai ke shirin dauka a wannan Talata wajen ladabtar da manyan kamfanonin sadarwar yanar gizo na duniya da ake zargi da amfani da karfin da suke da shi wajen danne takwarorinsu kanana da kuma kawar da kai kan bayanai da abubuwan da ake yadawa ta shafukan nasu.

Bayan share tsawon shekaru ana wasan buya sakamakon nuna yatsa da Turai ke yi kan laifukan kamfanonin sadarwar yanar gizon da suka hada da Google, Facebook da Amazon ke aikatawa a tsarin tafiyar da hamayyar kasuwanci a nahiyar Turai, kungiyar tarayyar turai EU ta sha alwashin kawar da matsalar.

A makon da ya gabata komishiniyar dake kula da kasuwancin cikin gida ta tarayyar turai uwargida Thierry Breton dakuma mataimakiyar shugaba a fanni hamayar kasuwanci Margrethe Vestager, sun sanar da cewa ya kamata turai ta tilasta amfani da tsare tsarenta wajen tabbatar da ikon tafiyar da komai a hannunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.