Faransa

Faransa na shirin karbar alluran rigakafin corona fin miliyan 3

Firaministan Faransa Jean Castex.
Firaministan Faransa Jean Castex. Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Gwamnatin Faransa ta ce za ta karbi maganın rigakafin cutar Corona sama da miliyan guda da dubu 160 nan da karshen wannan shekara, yayin da za a mika mata karin miliyan 2 da dubu 300 a watanni biyu na farkon shekara mai zuwa.

Talla

Firaministan kasar Jean Castex da ke sanar da hakan, ya ce cewa za a yi amfani da su wajen yiwa mutanen da suka fi hadarin kamuwa da cutar rigakafi, musamman masu shekaru da yawa da masu kula da marasa lafiyar.

Castex ya ce gwamnati za ta yi iya bakin kokarin ta wajen ganin anyi aikin bada allurar rigakafin a bayyane yadda jama’a za su gamsu, dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da tsananta a kasar dama sassan nahiyar Turai.

Zuwa yanzu dai manyan kasashen Duniya ciki har da Amurka da Birtaniya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiya sun amince da fara bai wa al'ummarsu rigakafin cutar ta Covid-19 wadda kawo yazo ta halaka mutane fin miliyan 1 da dubu dari 6 a sassan Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.