Amurka

Amurka ta amince da rigakafin COVID - 19 na kamfanin Moderna

Allurar rigakafin Covid - 19 na Moderna.
Allurar rigakafin Covid - 19 na Moderna. Photo AP / Hans Pennink

Amurka ta amince da allurar rigakafin cutar Covid 19 da kamfanin harhada magunguna na Modern ya samar don amfani da shi cikin gaggawa a kasar da annobar ke kashe sama da mutane dubu 2 da dari 5 duk rana.

Talla

Shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Stephen Hahn, ya ce duk da kasancewar alluran rigakafi har 2 a kasar, hukumarsa ta dauki wannan mataki mai mahimmanci don yakar annobar ne.

Amurka ce kasa ta farko da ta da ta amince da wannan allurar rigakafi da kamfanin moderna ya samar, wato ta biyu kenan da za a yi, amfani da ita a kasar, bayan na hadin gwiwar kamfanonin Pfizer da BioNTech.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.