Faransa

Guguwar Bella ta katse lantarkin sama da gidaje dubu 40 a Faransa

Yadda guguwar Bella ta murda igiyar teku kafin afkawa yankunan Normandy da Brittany dake Faransa
Yadda guguwar Bella ta murda igiyar teku kafin afkawa yankunan Normandy da Brittany dake Faransa AFP / FRED TANNEAU

Wata kakkarfar guguwa da masana suka lakabawa suna Bella ta katse layukan lantarkin akalla gidaje dubu 18 a yankunan Normandy da Brittany dake arewacin kasar Faransa.

Talla

Sai dai kamfanin lura da hasken lantarkin kasar na Enedis ya sake maida luyukan da guguwar ta katse.

A yankunan gabashi da tsakiyar Faransa kuwa guguwar ta Bella ta katse lantarkin wasu gidajen kimanin dubu 34.

Ma’aikatar lura da yanayin kasar tace guguwar ta Bella na tsala gudun kilomita 100 zuwa 120 a lokacin da ta afkawa.

Rahotanni sun ce akalla mutane 11 suka mutu sakamakon iftila’in guguwar, yayinda wasu dadama suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.