Wasanni

Dan kasar Argentina Mauricio Pochettino ya zama sabon kocin PSG

'Yan wasan PSG da tsohon kocinsu Thomas Tuchel
'Yan wasan PSG da tsohon kocinsu Thomas Tuchel Annegret Hilse/Reuters

Kungiyar kwallon kafa ta Paris SG ta tabbatar da dan kasar Argentina Mauricio Pochettino a matsayin sabon mai horas da yan wasanta kamar yadda aka yi hasashe tun farko.

Talla

Pochetino ya maye gurbin dan kasar Jamus Thomas Tüchel wanda kungiyar ta kora a farkon mako, inda ya samu kwantaragin shekaru biyu da kungiyar daga yanzu har zuwa 2022 da wanda kuma zai iya kara shekara daya idan da bukatar hakan.

Duk da kokarin da Touchel yayi na lashe kofuna da dama, rashin cin kofin zakarun turai da kungiyar ta buga wasan karshe ya zama babban kalubale a garesshi, saboda masu kungiyar sun kashe kudade da dama na tara masa yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.