Faransa-Coronavirus

Faransa tayi odar alluran rigakafin Coronavirus miliyan 8 na kamfanin Moderna

Faransa na shan caccaka kan tafiyar hawainiyar da shirin yiwa 'yan kasar alluran rigakafin cutar Korona ke yi.
Faransa na shan caccaka kan tafiyar hawainiyar da shirin yiwa 'yan kasar alluran rigakafin cutar Korona ke yi. Photo AP / Hans Pennink

Fiye da alluran rigakafin coronavirus na kamfanin Moderna dubu 50 ne suka isa Faransa da yammacin ranar Litinin wadanda za a fara amfani da su a yankunan da aka samu tsanantar cutar, musamman sabon nau’inta da ya yadu daga Birtaniya zuwa kasar ta Faransa.

Talla

Ministan lafiyar Faransa Olivier Veran ya ce tuni aka aike da wani kaso na alluran ga garuruwan Strasbourg dake kusa da iyakar kasar da Jamus da kuma birnin Nice dake gaf da gabar tekun Mediterranean, yankunan da cutar ke ci gaba da lakume rayuka.

Ministan ya ce za a fara yiwa jama’a alluran rigakafin a cibiyoyin da aka kebe daga ranar, inda ake sa ran shafe tsawon makwanni 12 ana tsikarawa jama’a alluran.

Faransa na sa ran karbar wasu alluran rigakafin miliyan 8 nan gaba kadan, ko da yake kasar na ci gaba da shan suka game da yadda aikin rigakafin ke tafiyar hawainiya.

A baya bayan nan Faransa da Tarayyar Turai suka amince da fara amfani da rigakafin na Moderna kari kan na hadakar Pfizer da BioNTech da suka fara amfani da su tun a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.