Jamus-Coronavirus

Adadin masu Coronavirus a Jamus ya haura miliyan 2

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce abin damuwa ne yadda cutar ke yaduwa cikin sauri a Jamus musamman sabbin nau’in na baya-bayan nan.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce abin damuwa ne yadda cutar ke yaduwa cikin sauri a Jamus musamman sabbin nau’in na baya-bayan nan. REUTERS

Adadin masu Coronavirus a Jamus ya zarta miliyan 2 dai dai lokacin da ake ci gaba da samun sabbin kamuwa da sabuwar nau’in cutar a sassan kasar.

Talla

Barazanar cutar na ci gaba da yiwa tattalin arzikin Jamus babbar illa musamman bayan da ta sake dawo da dokar kulle iyakokinta baya ga tilasta yiwa jama’a gwajin kwa-kwaf duk dai a kokarin dakile yaduwar cutar.

Kasashen Turai da suka kunshi Portugal da Birtaniya a bangare guda tuni suka dawo da dokar kulle baya ga tsananta yiwa jama’a allurar rigakafin Coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce abin damuwa ne yadda cutar ke yaduwa cikin sauri a Jamus musamman sabbin nau’in na baya-bayan nan.

Cikin jawabinta na jiya Alhamis shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce wajibi ne daukar tsauraran matakan dakile yaduwar cutar bayan samun sabbin kamuwa da cutar mutum dubu 22 cikin kasa da sa’o’i 24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.