Amurka-Honduras

Dubban 'yan Honduras da suka tunkari Amurka da kafa sun isa Gautemala

Dubban 'yan gudun hijira daga nahiyar tsakiyar Amurka a gaf da kasar Gautemala, yayin kokarin isa kasar Amurka. 21/10/2018.
Dubban 'yan gudun hijira daga nahiyar tsakiyar Amurka a gaf da kasar Gautemala, yayin kokarin isa kasar Amurka. 21/10/2018. Ueslei Marcelinov/Reuters

‘Yan Hunduras akalla dubu 3 ne suka fara tattaki da kafafunsu daga kasar da zummar zuwa Amurka don samun ingantacciyar rayuwa.

Talla

Ayarin dubban ‘yan Honduras din shi ne na baya bayan nan da ya fice daga kasar don gujewa matsin tattalin arziki, da tashin hankalin masu safarar muggan kwayoyi, bayaga masifun guguwa kashi biyu da suka afkawa sassan kasar.

Tuni dai ‘yan gudun hijirar da za su shafe dubban kilomitoci kafin isa Amurka, suka isa kasar Gautemala.

Dole ne kuma su gabatar da takardun izinin balaguro da shaidar gwajin cutar coronavirus, sharuddan da wasu ke ganin zai yi wuya dukkaninsu su cika.

A shekarar 2018, fiye da 'yan kasar Honduras dubu 7 suka yi tattaki zuwa Amurka, wadanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 1 bisa ukunsu kananan yara ne sai kuma tarin mata da suka mamaye ayarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.