Wasanni

Bilbao ta lashe Super Cup, yayin da aka kori Messi da jan kati

Dan wasan Barcalona da Argentina Lionel Messi.
Dan wasan Barcalona da Argentina Lionel Messi. REUTERS/Sergio Perez

An kori Lionel Messi a filin wasa a karon farko a Barcelona yayin da Athletic Bilbao ta baiwa club din na Catalan mamaki wajen lashe gasar Super Cup na Spain.

Talla

A ranar Lahadi aka fafata wasan karshe mai cike da mamaki bayan da Athletic ta doke Barcelona 3-2 bayan karin lokaci.

'Yan lokuta kafin nasarar Bilbao, anga Messi na wurga hanu ga Asier Villalibre, wanda ya ci kwallo a mintuna 90 da ya hanawa Barca nasaran kwallaye biyu da Annonie Grizman ya zura a ragar Bilbao, abin da yasa aka tsawaita lokacin wasa, kuma Inaka William ya ciwa Bilbawo kwallo na 3 da ya basu nasarar lashe kofin.

A kokarin Barca na neman nasara a wasan ne aka bar Messi ya buga wasa har na tsawon mintuna 120, kafin ya huce haushinsa kan dan wasan Bilbawo da ya farke kwallon su, matakin da ya kai ga bashi jan katin kora daga fili, karon farko a wasanni 753 da ya bugawa Barca, kari kan biyu na Agentina da ya samu a shekarar 2005 da 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.