Birtaniya da Faransa sun kara kaimi wajen rigakafin Covid -19

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, rike da allurar rigakafin Covid 19 da kamfanin Astra zaneca ya samar
Firaministan Birtaniya Boris Johnson, rike da allurar rigakafin Covid 19 da kamfanin Astra zaneca ya samar Paul Ellis/Pool via REUTERS/File Photo

Faransa da Birtaniya sun bi sahun jerin kasashe wajen kara kaimi a gangamin rigakafin coronavirus wanda a wannan karon zai shafi dattijan da shekarunsu ya fara daga 50 zuwa sama, yayinda Birtaniya ta sanar da kulle wasu iyakokinta baya ga sanya dokar killace kai ga ilahirin bakin da suka shigo mata a kokarin dakile yaduwar Covid-19.

Talla

A cewar ministan da ke jagorantar aikin rigakafin a Birtaniya Nadhim Zahawi, za a sake tsaurara matakai kan wadanda ke shigowa kasar yayin da rigakafin zai shafi hatta wadanda shekarunsu ya kai 70 a Duniya.

A bangare guda, Stephen Powis, daraktan hukumar Lafiyar kasar ya ce alkaluman wadanda za a yi wa rigakafin ya karu zuwa mutum miliyan 5, alkaluman da ke matsayin kari kan mutane miliyan 3 da dubu dari 8 da suka karbi allurar rigakafin zagayen farko da aka faro a watan Disamban bara.

Zuwa yanzu fiye da mutum dubu 89 coronavirus ta kashe a Birtaniyar, yayin da ta harbi mutane miliyan 3 da dubu dari 4.

A bangare guda, Faransa ta kara yawan wadanda za su fara karbar sabon rukunin allurar rigakafin wanda zai faro daga kan ‘yan shekaru 75, matakin da ke zuwa bayan kasashen da cutar ta fi gallaba irinsu Birtaniyar, Brazil da kuma India sun kaddamar da gagarumin gangamin allurar.

Ministan lafiyar kasar Olivier Veran, ya ce a cikin watan janairu kadai za a yi wa Faransawa miliyan 1 zuwa miliyan 2 da rabi allurar rigakafin, yayin da za a yi wa wasu miliyan 4 a cikin watan Fabarairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.