Wasanni

Muna jinjinawa mai tsaron ragarmu duk da rashin nasara - Liverpool

Mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker
Mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker Liverpool.FC

Manchester United ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar Premier Ingila da maki uku a kan Liverpool dake rike da kambin gasar, bayan canjaras din da sukayi da ita, to sai dai jarumtakar da mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker ya nuna ya hanata gagarumin nasara da ya bayyana a Anfield.

Talla

Liverpool ta ci gaba da kasancewa ta hudu a kan teburi, bayan da ta gaza yin nasara a wasanni uku a jere na gasar, amma ta na mai jinjina ga golanta dan kasar Brazil da tsawaita wasanni 68 wanda ta buga a gida ba tare da an doke ta ba a gasar Premier, bayan da ya hana Bruno Fernandes da Paul Pogba harin da sukayi ta kaiwa.

United ma dai, wasanni 12 ta yi ba a doke ta ba a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.