Faransa-Islam

Macron ya yabawa Musulmin Faransa kan amincewa da dokar yaki da tsaurin addini

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AP News

Shugaba Emmanuel Macron ya yaba da matakin shugabancin kungiyar Musulmin Faransa dangane da amincewarsu kan dokar ‘‘charter of principles’’ da za ta yaki tsattsauran ra’ayin addinin Islama.

Talla

Shugaba Macron a wata sanarwa da Ofishinsa ya fitar ya ce manufar sabuwar dokar bai wuce cire zafin akida daga zuciyar musulman ba, wanda ke da alaka da hare-haren ta’addanci na baya-bayan da kasar ta gani.

Bayan wata ganawa da shugabancin kungiyoyin Musulmin na Faransa, Macron ya ce matakin da suka dauka abin a yaba musu ne wanda kuma zai taimakawa kasar yakar ayyukan ta’addanci wadanda gwamnatin Paris ta yi imanin suna da alaka da tsattsauran ra’ayi ko kuma zafin aqida daga mabiya addinin na Islama.

A yammacin jiya Litinin ne shugabancin kungiyar Musulmin Faransa ya amince da kudirin Macron na samar da sabbin tsare-tsare a kokarin yaki da tsattsauran ra’ayi da kuma zafin aqida, ko da ya ke sai da aka kai ruwa rana tsakanin jagororin musulmin wajen sauya wasu dokokin Islama domin su yi dai dai da kundin tsarin mulkin Faransar.

A zantawarsa da manema labarai, shugaban kungiyar musulmin ta Faransa Mohammed Moussaoui ya ce dokokin yaki da tsattsauran ra’ayin 10 da gwamnatin Faransar ta gabatar musu ba su yi hannun riga da koyarwar addinin Islama ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.